JSS1 Hausa Language Past Questions- 2nd Term Session
						JSS1 Hausa Language Past Questions- 2nd Term academic Session. Get complete guides aim Hausa scheme of work, lesson notes and plan for studies.
HAUSA LANGUAGE SCHEME OF WORK
MAKO BATU
Bita akyyukan sashen daya gabata
Ma’anar rubutaccen adabi (maimaitawa)
Rukunonin rubutaccen adabi
Tsarin rubutaccen adabi
Ma’anar sana’a
Muhimmancin sana’a
Ire-iren sana’o’i
Bayanin wadansu zababbun sana’o’i
Hanyoyin Kyautata sana’o’i
Mako na Daya(week 1) Bita akyyukan sashen daya gabata (Revision)
Mako na biyu (Week 2)
Batu (Topic) Ma’anar rubutaccen adabi:
Ma’anar rubutaccen adabi shine adabin zamani. Ana kiran wannan adabi ‘Rubutaccen adabi’ saboda da can can, tun asali, a rubuce ake tsara shi. Kuma ana kiransa ‘Adabin zamani’ Saboda bai dade sosai da shigowa ba kamar adabin gargajiya. Rubutaccen adabi ko adabin zamani ya samu ne bayan da hausawa suka iya rubutu da karatu. Hausawa kuwa, ga alama ba su iya karatu da rubutu ba sai bayan da musulinci ya shigo kasar hausa da kuma bayan turawa suka zo.
Musulinci ya shigo kasar hausa ta hannun larabawa da mutanen melle. Shi ko musulinci yana amfani da harshen larabci. Don haka da musulinci ya shigo kasar hausa, sai hausawa suka koyi rubutu da karatu irin na larabci. A hankali a hankali kuma suka kirkiro rubutun hausa da harufan larabci. Ana kiran irin wannan rubutu da sunan “Rubutun Ajami” Da rubutu ajami ne hausawa suka fara rubuta wakokin addinin musulinci da hausa.
Daga baya turawa suka shigo kasar hausa suka kafa mulkin mallaka. Su ma da suka zo sun taimaka wa hausawa wajen kirkiro rubutun boko. Shi kuma rubutun boko yana amfani da haruffan turawa. Da aka sami rubutun boko kuma sai aka shiga rubuce-rubucen littattaffan labarai, littattaffan koyon karatun boko, da wasan kwaikwayo, da sauransu.
3. Mako na uku (week 3)
Batu (Topic) Rukunonin rubutaccen adabi
Rubutaccen adabi ya rabu zuwa gida uku, kamar haka :-
Rubutun wakoki
Wadannan su ne wakokin da aka rubuta da ajami. Wadannan wakoki da aka rubuta da boko, wadanda bayan addini, suna kuma magana a kan harkokin duniya.
b) Rubutun Zube
Wannan shi ne rubutu wanda aka yi shi ba cikin tsarin waka ba, misali kagaggun larabai wadanda ake karantawa don nishadi da kuma koyon zaman duniya da wasa kwakwalwa. Su wadannan labarai yawancisu littattafai ne wadanda ana fara yin su ne bayan da turawa suka kafa mulkin mallaka kuma hausawa sun iya karatu da rubutun boko.
c) Wasan Kwaikwayo
Wadannan wasanni ne da ake shiryawa a rubuce. Akwai kuma wasan kwaikwyon da ake shiryawa a rubuce don rediyo, akwai na talebijin , akwai kuma wanda ake yi a dandamali don yan kallo su gani.
Rabe-raben Rubutaccen Adabi
Kowane dan adam da irin baiwar da allah ya yi masa a kan kusan kowace harka ta rayuwa. A fannin adabi haka abin yake, cewa wadansu Allah ya yi masu baiwar nuna fasaharsu ga al’umma a wannan bangare ta hanyar rubutu. Ta rubutun ma akwai inda kowanne yake irin ta sa baiwar. Dangane da wannan akwai kashi uku na nau ‘o’ in rubutaccen adabi.
Na farko dai akwai wadanda su ke da baiwar iya shirya labari, Wato ta irin wadannan labarai suke nuna fasaharsu ta ba da nishadi da kumma hannunka mai sanda ga al’umma. Irin wannan nau’i na rubutaccen adabi ake yi wa lakabi da zube. Don haka Zube bangare ne na rubutaccen adabi.
Na biyu kuwa shi ne irin wadannan da ke da baiwar iya waka. Kamar zube waka ma ta hanyarta akan sami nishadi da kuma hannuka mai sanda. Ita ma dai wani bangare ne na rubutaccen adabi.
Na uku kuwa shi ne Karaminsu a duniyar Hausawa, wato rubutaccen wasan kwaikwayo. Wajen bambance shi da irin wasan kwaikwayo na asali na hausawa, sai aka yi masa lakabi da wasan kwaikwayon zamani. Don haka wasan kwaikwayo na zamani ma bangare ne na rubutaccen adabi a al’ummar hausawa
Amfanin Rubutaccen Adabi
Adabi a rubuce ko kuma azanci a rike da kowanne ciki akan sami nishadi ta karanta shi ko kuwa sauransu. Saboda haka nishadi na daga cikin irin amfanin da ake samu daga rubutaccen adabi. Bayan nishadi kuwa wani babban amfanin adabi shi ne isar da wani sako na musamman. Irin wannan sako kuwa daga tunanin mawallafin wannan adabin ne yake.
Wani babban amfanin rubutaccen adabi kuwa shi ne adana shi adabin. Wato a nan, ba kamar azancin da ke ka ba, muddin dai abu a rubuce yake, to ba za a sami ragi da kari ba. Yadda aka rubuta shi, komai dadewar zamani idan ak dauko shi, za a tarar cewa yadda aka ajiye shi haka za a same shi wato ba dadi ba ragi.
Auna fahimta:
Menene rubutaccen adabi?
Lissafa rukunonnin adabi guda uku (3)
Mako na Hudu:
Batu(Topic): Tsarin Rubutaccen Adabi
Rubutaccen adabi kamar yadda mukayi bayyani shi ne wanda ake kira da ‘Adabin zamani’ wannan shi ne adabin da masu ilimi suka rubuta a littafai don jama’a su karantasu kuma amfana.
Ilimin rubutu, wato yin amfani da tsara wadansu alamomi a kan takarda ko wadansu abubuwa, kamar allo, ganye dutse da makamantansu don sadar da wata magana ko sako, wacce dan Adam ya saba da fadar ta da fatar baki, a kuma saurare shi da kunne, ya samu ne ga dan Adam lokaci mai tsawo, kuma dan Adam yana yin amfani da alamomin rubutu iri-iri a sassa daban-daban na duniya. Misali mutanen kasar China (sin) suna yin amfani da wadansu alamomi masu kama da zane, ko hoto don sadar da magana a rubuce tun shekara 3,500 da suka wuce. Su kuma Jafanawa mutanen kasar Japan, suna yin amfani da wata alama guda daya tak ta wakilci gabar kalma, wato ta yi aikin baki da wasali wajen rubutu magana tun kimanin shekaru 2,000 da suka wuce.
Hausawa sun dauki irin tsarin alamomin da turawa da larabawa suke yin amfani da su. Wato alamomin nan na “abacada” suna rubutu maganarsu ta hausa da su. Watau hausawa, sun yi amfani da tsarin alamomin rubutu na Larabawa wajen maganganunsu, wannan irin tsari shi suke kira da “Rubutun Ajami”. Haka kuma, sun yi amfani da tsarin rubutun turawa na abacada, wajen rubuta maganarsu ta hausa, wannan shi suke kira da “Rubutun boko”.
Hanyoyin Nazarin Rubutaccen Adabi
A wajen nazarin rubutaccen adabi, wato zube (labari) ko wasan kwaikayo, ko waka, ana yin la’akari da wadannan muhimman abubuwa:
Zubi da tsari
Jigo
Bayyanin Jigo
Warwarar Jigo
Salon sarrafa Harshe
A wajen nazarin rubutaccen waka, tilas ne a kulla da wadannan abubuwa guda biyar a kan kowane bangaren rubutaccen adabi Ga misali:
Zubi da tsari: Mai yin nazarin zai yi kokari ya fito da yadda marubucin wakar ya tsara ta, wato ya kula da yadda aka fara bude wakar, ko marubucin ya fara da addu’ar budewa, ko bai fara ita ba. Mafi yawan rubutattun wakokin Hausa suna farawa ne da addu’ar budewa, inda ake neman taimako daga Allah ya dada ba da basira, da kuma yabon Annabi, kamar yadda malam sa’adu Zungur ya yi a farkon wakarsa ta Bidi’a inda ya ce:
“Ka daura niyya a kan waka kana addu’a
A’uzu Billah daga shaidan a kan bida’a.
2.Sannan kawo basmala bisa kan rikon sunna,
Ka biya da yin hamdala ita ce wajen jama’a
3.Dafa kawo salsala don kammala da’a
Ga wanda aikensa rahama ce wajen jama’a
4 Ka iyar da kalmar salatu zuwa ga Alaye,
Da sallama ga sahabbai masu kyan dara’a
Wannan ita ce ake cew addu’ar budewa. Sai kuma a kula da yadda marubucin ya rufe ita wakar, wato ko ya rufe ta da addu’a, ko kuma da bayyana sunansa a karshe.
(ii) Jigo: Jigo Dai shi ne manufar waka, watau sakon da take dauke da shi a dunkule. A wajen nazarin waka, wajibi ne a gano jigon wakar a fito da shi a fili, a kuma fito da baiti ko a bayyana yadda mawakin ya gina jigon nasa a cikin baitocin wakar. Daga nan sai warwarar jigo, ana ne mai nazari zai yi kokari ya bayar da tasa fahimtar a kan jigon wakar, yana yin sharhi sosai tare da kowa misalai daga wakar. Idan an zo wajen nazarin waka za a ga misalai na yadda ake fito da jigo, da kuma warwarar jigo a nan gaba, cikin littafi na biyu.
Salon sarrafa Harshe: A nan za a yi la’akari da yadda marubucin waka yayi amfani da harshe, ko yan da saukin fahimta ko ya yi wahala. Sannan kuma za a kara kula da yawan kalmomin aro na wasu harsuna kamar
Larabcida turanci da marubucin ya yi amfani da su a cikin wakar. Da irin yadda ya nuna gwanintar harshe a cikin wakar ta wajen yin amfani da karin magana, da kirari. Sai kuma a lura da yadda marubucin yayi amfani da “lugogin Harshe” wato irin dabarun jawo hankali, kamar su:
Siffantawa
Kamantawa/Misaltawa/kwatantawa
Mutuntawa
Karagiya/Luguden kalmomi
Auna Fahimta
Wajen rubutaccen adabi, bada muhimman abubuwan da ake la’akari da su?
Yi bayani daya daga cikin su.
Tarihin rubutun hausa
				

